4 Janairu 2026 - 13:27
Source: ABNA24
Sojojin Amurka Suna Sabbin Yunkuri A Iraki Da Siriya

Wata majiyar tsaro ta Iraki ta ba da rahoton motsin manyan motoci kimanin 150 dauke da sojojin Amurka da kayan aikin soja daga sansanin Ain al-Assad da ke yammacin lardin Anbar zuwa sansanin Al-Tanf da ke Siriya da kuma sansanin Harir da ke Erbil.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Wannan motsi ana daukarsa a matsayin ci gaba da yunkurin sojojin Amurka a yankin kuma yana iya zama alama ta karuwar shirye-shiryen soja na Washington a ciki da wajen Iraki.

Your Comment

You are replying to: .
captcha